SiyasaAfirka
Koriya ta Arewa na kisan mutane a asirce
December 16, 2021Talla
Wata kungiyar binciken take hakkin dan Adam da ke a Koriya ta Kudu, Transitional Justice Working Group ce ta bankado wannan zargin. Kungiyar ta ce ta samu cikakkun bayanan hakan a wurin wasu mutane da suka tsere daga Koriya ta Arewa, inda suka shaida mata cewa kimanin mutane 23 gwamnatin Shugaba Kim Jong Un ta halaka a bainar jama'a a cikin shekaru 10 da Kim Jong Un ke mulki.
Sai dai tuni Koriya ta Arewan ta yi watsi da zargin, tana mai siffanta hakan a matsayin kokari na bata mata suna ta hanyar goga mata laifin take hakkin bil Adama. To amma an jima ana zargin gwamnatin Kim Jong Un da kashe 'yan kasar ciki har da manyan jami'an gwamnati a gaban jama'a, a wani mataki na razana 'yan kasar da ke da mabanbantan ra'ayoyi da hukumomi.