1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa na fuskantar yunwa

May 3, 2019

Akalla 'yan kasar Koriya ta Arewa miliyan 10 ne ke fuskantar karancin abinci, sakamakon tsananin rashin samun amfanin gona da manoma suka yi a bana.

https://p.dw.com/p/3HuQi
Nordkorea Hunger Trockenheit
Hoto: AP

Hukumar abinci ta duniya, ta ce karancin abincin a Koriya ta Arewa, na da nasaba ne da sauyin yanayi da ya haddasa fari da ambaliyar ruwa, sai kuma karancin man fetur da takin zamani da manoma suka fuskanta.

Wani bangaren matsalar kuwa ya hada har da takukuman da kasar ta gani, saboda neman tilasta wa Shugaba Kin Jong-Un, jingine nuna karfi da yake yi na mallakar makaman nukiliya.

Matsalar kuwa ta fi zafi ne a rayuwar kananan yara da mata masu shayarwa da ma wadanda ke dauke da juna biyu.