1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami

Binta Aliyu Zurmi
October 28, 2022

Rahotanni daga Koriya ta Arewa na cewar da saynin safiyar wannan Juma'ar ta harba makamai masu linzami da ke cin matsakaicin zango a gabar tekun a wani gwaji da ta yi.

https://p.dw.com/p/4ImlU
Hoto: Yonhap/picture alliance

Wannan sabon gwajin makaman dai na zuwa ne bayan tsahirtawa da kasar ta yi na kusan makwanni biyu. 

Tuni dakarun sojin Koriya ta Kudu suka tabbatar da wannan gwajin da ya sauka a gabashin tekun kasar. Sojin Amirka sun gargadi Koriya ta Arewa bisa amfani da makamai masu linzami, matakin da suka ce ka iya kawo karshen wannan gwamnatin. 

A makon da ke tafe ne Koriya ta Kudu za ta gudanar da wani atisayen kawance da sojojin Amirka da ya kunshi jiragen yaki na musamman samfurin F-35 140 daga Koriya da kuma wasu 100 daga Amirka, a cewar ministan tsaron Koriya ta Kudu .

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jima yana gargadin Koriya ta Arewa bisa gwaje-gwajen da take yi da a wasu lokutan ma ta kan harbasu ga kasashen da ke makwabtaka da ita.