1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa da ta Kudu za su tattauana

Ahmed SalisuJanuary 1, 2015

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce kasarsa za ta tattauna da takwararta Koriya ta Kudu da suka shafe shekaru suna zaman doya da man ja.

https://p.dw.com/p/1EDmO
Kim Jong Un mit Stock 14.10.2014
Hoto: Reuters/KCNA

A sakonsa na sabuwar shekara ga al'ummar kasarsa Shugaba Jong-Un na Koriya ta Arewan ya ce tattaunawa za ta gudana ne bayan nazari kan yanayin da ake ciki, inda a hannu guda ya ce ya kyautu a kawar da tsamin dangantakar da ke akwai tsakanin Koriyoyin biyu.

Tattaunawar da za ta gudana dai za ta kasance irinta ta farko a shekaru bakwai din da suka gabata kuma hakan na zuwa ne daidai lokacin da mahukuntan Pyongyang ke shan matsin lamba daga kasashen duniya saboda zargin tauye hakkin bani adama da ake musu.