Koriya ta Arewa da sake yin gwajin makami
January 27, 2022Dama dai Koriya ta Arewa ta yi barazanar sake yin gwajin makami mai linzami. Sai dai rabon ta yi gwajin makamai masu yawa a cikin wata guda tun shekarar 2019, bayan wargajewar tattaunawar tsakanin shugabanta Kim Jong Un da shugaban Amirka na wancan lokaci Donald Trump.
Wannan jerin gwaje-gwajen makamai da aka haramta ya haifar da tofin Allah tsine a duniya yayin wani taron sirri da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar. Ita ma Amirka ta kakaba wasu sabbin takunkumai a matsayin martani, lamarin da ya harzuka Koriya ta Arewa.
Wadannan gwaje-gwajen makaman sun zo ne a wani yanayi mai sarkakiya a yankin, inda babbar kawar Koriya ta Arewa wato Chaina ke shirin karbar bakuncin gasar Olympics na lokacin sanyi a watan Fabrairu, yayin da Koriya ta Kudu na gudanar da zaben shugaban kasa a watan Maris.