1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Koriya za su sake kulla alaka

July 27, 2021

Kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta kudu sun sanar da sake maido da wasu hanyoyin sadarwarsu, a wani mataki na sake kulla alaka tsakanin shugabanin kasashen biyun.

https://p.dw.com/p/3y6jV
Nordkorea | Pjöngjang | Parteikongress | Kim Jong-un
Hoto: AFP

Tun dai a watan Afrilun da ya gabata ne dai shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in da takwaransa Kim Jong Un suka yi musayar wasiku kan cimma matsayar maido da layukan sadarwar kasashen. 

Kamfanin dillancin labaran kasar Koriya ta Arewa ya ce hakan wata hanya ce ta sulhu da kuma aminci tsakanin kasashen biyun. Wannan matakin dai na zuwa ne a yayin da kasashen ke cika shekaru 68 da kawo karshen yakin Koriya.

Tun dai a watan Yunin shekarar 2020 ne dai Koriya ta Arewa ta katse hanyoyin sadarwarta bayan da shugaba Moon ya bukaci yin sulhu tsakanin takwaransa da tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump, lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.