1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba da harba makami mai linzame

Abdoulaye Mamane Amadou
August 6, 2019

A wani mataki na nuna damuwa kan atisayin sojan hadin gwiwa na Amirka da Koriya ta Kudu, Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami karo na hudu a kasa da mako biyu.

https://p.dw.com/p/3NOkF
Nordkorea unternimmt neue Waffentests
Hoto: picture-alliance/dpa/kcna

Koriya ta Arewa ta yi barazanar ci gaba da gwajin makamanta masu linzami biyo bayan harba wani makami mai cin dogon zango da ta yi a matsayin gwaji karo na hudu da ta yi kasa da kwanaki 12.

Tsawaita gwajin makaman na Arewan na zuwa ne a daidai lokacin makwabciyarta Koriya Ta Kudu da Amirka ke wani atisayin soja, atisayin da gwamnatin Pyongyang ta kira babbar barazana kana hukumomin na Koriyar suka ce hakan na iya dagula matakan da ake dauka, na kwance damarar kasar ta fuskar diflomasiya da manyan kasashen duniya suka fara tunkara ciki har da kasar Amirka tun a shekarar 2018.