1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Libiya: Tisa keyar 'yan ci-rani Nijar

August 7, 2024

'Yan ci-rani sama da 1,500 ne suka ya da zango birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar, bayan da a karon farko mahukuntan Libiya suka tasa keyarsu gida.

https://p.dw.com/p/4jD76
Jamhuriyar Nijar | Agadez | 'Yan Ci-rani | Libiya
Ba yanzu ne dai 'yan ci-rani ke kwarara daga ksashe da dama zuwa Libiya baHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Kafinn isar 'yan ci-ranin birnin na Agadez na Jamhuriyar Nijar din, sun tagayyara a Libiya. Tarihi dai ya nunar da cewa akwai dangataka mai kyau tsakanin Libiya da Jamhuiyar ta Nijar, kuma ba a taba samun Libiya ta koro 'yan ci-ranin Nijar da ke zuwa kasar domin neman kudi tare da tafiyar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali da lumana ba. Sai dai kwatsam an wayi gari Libiyan ta isa keyar 'yan Nijar din gida. Koda yake sun samu kulawa ta musuman daga hukumomin Nijar, tun daga kan iyakar kasar da Libiya. 'Yan ci-ranin da suka kasance matasa na fatan samun ayyuka a gida Nijar din, domin rashin aikin yin ne ke sanya su yin wadannan tafiye-tafiye. Bayan kasar Aljeriya da ta dade tana koro 'yan Afirka, sai dai kuma Libiya ita ma ta bi sawu wajen fara koro 'yan Afirkan gida. Koda yake mahukuntan Nijar a wanan karon, sun taka muhimmiyar rawa wajen mayar da 'yan ci-ranin da aka koro garuruwansu na asali.