1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu zai ci gaba da mahawara kan Siriya

August 3, 2011

Al'ummomin ƙasar Siriya na ci gaba da gudanar da gangamin adawa da kyamar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad

https://p.dw.com/p/12AA3
Hoto: dapd

A yau laraba ne komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai ci gaba da tattaunawa akan halin da ake ciki na ƙaruwar boren adawa da Gwamnati a ƙasar Siriya.

Wakilan komitin 15 a jiya talata sun gaza cimma  matsaya dangane da kalmar nan ta yin "Allah wadan matakan shugaba Bashar al-Assad" na kamen 'yan adawa da ake ci gaba da yi sakamakon gangami da zubar da jinin al'ummar ƙasar. Ƙasashen yammaci na turai na kira da a ɗauki tsauraran matakai, a yayinda China da Rasha suka yi barazanar hawa kan kujerar na ƙi dangane da kowane mataki mai tsauri aka ɗauka a hukumance. A kwanaki ukun da suka gabata dai, mutane 137 ne aka kashe a zanga-zangar ƙasar ta Siriya. A birnin Hama kaɗai dai mutane 93 ne suka rasa rayukansu, sakamakon somame da tankunan sojin Siriya suka kai a garin a ranar lahadi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Umaru Aliyu