1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wanzar da zaman lafiya a Afganistan

July 8, 2019

Kasar Jamus da hadin gwiwar kasar Qatar sun gayyaci kungiyar Taliban da sauran masu dauke da makamai a kasar Afganista, izuwa taron sasantawa a birnin Doha, domin duba makomar Afganistan da rikici ya dai-daita.

https://p.dw.com/p/3Ll1V
Abdul Salam Zaeef babban jami'i Taliban lokacin a gaban manema labarai a taron sasanta 'yan Afganistan a birnin Doha
Abdul Salam Zaeef babban jami'i Taliban lokacin a gaban manema labarai a taron sasanta 'yan Afganistan a birnin DohaHoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

Wannan dai shi ne karon farko da za a yi zaman gaba da gaba tsakanin gwamnatin Afganistan da kungiyar Taliban. Da ma dai kungiyar Taliban ce ke adawa da zaman teburi guda tare da gwamnatin Kabul.

Gwammai na mata da maza 'yan kasar ta Afganistan za su yi zaman sulhu a Doha, sai dai kawo yanzu ba a bayyana ainihin dukkan wakilan da aka gayyato daga Afganistan a zaman da za su yi da Taliban ba. Rainer Breul shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus, kasar da ke daukar nauyin sasantawar da za a yi. Ya bayyana abu muhimmanci a wannan zaman sulhun na Doha.

"Abin bukata shi ne ba da dama ga kungiyoyi dabam-dabam na kasar don hada kansu. Kuma an dauko kungiyoyin daga yankunan kasar dabam-dabam daga cikin kasar ta Afganistan."

Abu mafi muhimmanci dai wannan zaman sasantawa a karon farko ya faru. Domin tun a watan Afrilu aka shirya zaman tsakanin Taliban da gwamnatin Afganistan da sauran kungiyoyin farar hula na kasar amma hakan bai samu ba.  Kasar Amirka dai tun watanni ta fara tattaunawa da Taliban, to amma duk ana yi ne tsakaninsu da Taliban ba tare da gwamnatin Afganistan ba. Ga kunguiyar Taliban irin wannan zaman da Amirka bai da amfani don haka suke bukatar zama da gwamnatin Afgnistan.

Suhhail Shaeen kakakin Taliban a Qatar, wanda kuma ke halartan taron na birnin Doha
Suhhail Shaeen kakakin Taliban a Qatar, wanda kuma ke halartan taron na birnin DohaHoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

To amma a cewar gwamnatin Afganistan zaman da za a yi tamkar bata lokaci ne domin an sanya sharadin cewa duk wanda zai wakilci gwamnatin Kabul zai zo ne a matsayinsa na mai zaman kansa amma ba bisa mukaminsa na minista ko wani abu ba. To sai dai a cewar Abdullah Qarluq wani sanatan Afganistan, da shi ma zai halarci taron na Qatar duk wadannan ba sune abin ji ba.

"Wannan zaman yana ba mu fatan samun zaman lafiya. Al'ummar Afganistan na fatan ganin an samu zaman lafiya tun gomman shekaru. Sai dai tun da jimawa iya bukatun Amirka da 'yan Taliban kawai ake magana, bukatun al'ummar Afganistan an jingine su a gefe. A wannan zaman muna son fada musu zahirin abin da 'yan Afganistan ke so wa kasarsu."

Matan Afganistan da ke zaman dirshan a Kabul suna adawa da magudin zabe
Matan Afganistan da ke zaman dirshan a Kabul suna adawa da magudin zabe Hoto: DW/G. Adeli

Shin ya Afganistan mai zaman lafiya ya kamata ta kasance? Demokradiyya za ta ci gaba da wanzuwa a kasar? Mata za su ci gaba da samun karatu suna rike mukaman siyasa? Kuma wane irin tsari kasar za ta bi wajen bai wa jama'a hakkinsu? Wadannan suna cikin tambayoyin da zaman sulhun zai tattauna. To sai dai har yanzu Taliban na ci gaba da yakar gwamnati da sojojin mamaya. Ga kasar Amirka dai watakila abin da take son cimma shi ne, a nan gaba kada a bar wasu 'yan ta'adda su koma can da zama, kuma a nan bukatar shata lokacin da sojojin kasashen waje za su fice daga Afganistan. Hamid Saboori masanin siyasa ne a kasar Afganistan, wanda shi ma ya ce zaman taron na da alfanu.

"Ko da kuwa masu halartan taron ba da sunan gwamnatin Afganistan za su halarta ba, amma dai suna dauke da ra'ayin gwamnatin kasar ne. Hakan dai wata alama ce cewar Taliban na son magana da gwamnati. A karshe dai an kawar da babban abin da ke kawo cikas. Don haka wannan zaman na da matukar muhimmanci."

Duk da cewa kasashen Jamus da Qatar suka gayyoto masu halartan taron, amma kuma za su bar 'yan Afganistan zu tattauna su ya su, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta tabbatar.