1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance matsalar ‘yan gudun hijira

Mohammad Nasiru Awal
March 18, 2020

Shugabannin Jamus da Faransa da Birtaniya sun tattauna da shugaban Turkiyya ta hanyar bidiyo domin samo masalaha kan batun 'yan gudun hijira da ke iyakar Turkiyya da kasar Girika.

https://p.dw.com/p/3ZeNS
Türkei Bundeskanzlerin Merkel zu Besuch in Istanbul
Hoto: AFP/M. Kula

A makon da ya gabata ba tare da ya ce uffan ba, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bar birnin Brussels gabanin taron manema labarai bayan wata ganawa da shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen da shugaban majalisar kungiyar EU Charles Michel. A ranar Talata ya kamata wata tawagar Turai ta tafi birnin Santambul don tattaunawa da shugaban na Turkiyya kan yakin Siriya, amma saboda annobar cutar Corona hakan ba ta samu.

Griechenland Auf Schiff festgehaltene Migranten zum griechischen Festland gebracht
Wasu 'yan gudun hijira a iyakar kasar GirkaHoto: picture-alliance /AA/A. Mehmet

Sai dai an tattauna ta fasahar bidiyo tsakanin Erdogan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da kuma Firaminista Boris Johnson na Birtaniya. An jiyo Erdogan na cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan mawuyacin halin da ake ciki a yankin Idlib na kasar Siriya.

Ita ma Merkel ta ce tattaunawar ta yi amfani, tana mai cewa ba a kawar da yiwuwar karin taimako daga EU ga Turkiyya ba, sannan Turkiya ta ce za ta ci gaba da zama mamba a kungiyar NATO.

A karshen watan Fabrairu Turkiyya ta bude kan iyakarta da EU, matakin da ya ba wa dubban 'yan gudun hijira kama hanyar shiga kasashen EU, amma 'yan sandar kasar Girika suka dauki matakan ba sani ba sabo kansu. EU da kungiyoyin kare hakin dan Adam sun zargi Turkiyya da amfani da batun 'yan gudun hijira don cimma bukatunta.