1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin hana yaki a nahiyar Turai

Abdourahamane Hassane
February 9, 2022

Kasashen Faransa da Jamus da Poland su hada kansu a yunkurinsu na hana afkuwar yaki a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/46j6H
Berlin Weimar Triangle Duda Scholz und Macron
Hoto: HANNIBAL HANSCHKE/REUTERS

Shugabannin kasashen guda uku wadanda suka gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Cholz a birnin Berlin sun ce ba za su bari ba a shiga yin yaki da Rasha. A lokacin da yake magana da manema labarai bayan tattaunawarsu da shugabanin Faransa da kuma Poland shugaban gwamnatin Jamus Olaf Cholz ya ce za su yi ruwa su yi tsaki a kan wannan batu har sai sun tabbatar da zaman lafiya  a tsakanin Ukraine da Rasha.