Kwararru na WHO na kokarin hana yaduwar Ebola
May 20, 2018Tuni aka kebe wadanda suka kamu da cutar kuma ake kula da su a babban asibitin Wangata da ke tsakiyar birnin Mbandanka, birnin da ke da jama'ar da yawanta ya kai mutum miliyan daya da dubu dari biyu. A cewar Docta Hilaire Manzibe, babban daraktan wannan asibitin da ake kula da 'yan malatin na Ebola, lalle ba za su iya bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar da a yanzu aka killacesu ba, amma suna sanar da cewa an samu wadanda suka mutu, kuma sauran wadanda ake kula da su na da alamun samun sauki.
Sai dai babban likitan ya ce abin damuwar ma a nan shi ne yana tune a ranar daya ga watan Mayu an kawo wani mai zazzabi kuma yana amai, amma danginsa suka nemi da a ba su shi su yi masa na gargajiya.
A halin yanzu dai duk wasu da suka yi mu'amula da masu dauke da cutar an killacesu har na tsawon lokaci.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta aike da wata tawagar kwararru guda 35 da suka kware wajen allurar rigakafi, kuma 16 daga cikinsu sun taka rawar gani a lokacin yaki da annobar cutar ta Ebola da aka fuskanta a wasu kasashen yammacin Afirka.