1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin Afirka na tura kwararru Burundi

Ahmed Salisu
September 28, 2017

Wasu kasashen Afirka da ke Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da wani kuduri da ya bukaci aikewa da kwararru na Majalisar don su gudanar da bincike kan zargin cin zarafin al'umma da ake yi wa hukumomin Burundi.

https://p.dw.com/p/2kvEU
nach Putschversuch - Präsident Pierre Nkurunziza zurück im Amt
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Wannan bukata ta kasashen ta biyo bayan fitar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya nuna irin yadda aka kashe mutane tare da azabtar da wasu wanda aka jingina yin hakan ga mahukuntan Bujumbura. Kasashen dai na son ganin kwararrun da za a tura su tantance zargin da ake yi wa gwamnati ta hanyar tattara bayanai kana su yi aiki da jami'an gwamnatin kasar da nufin rarrabe tsaki da tsaba. Kudurin ya samu amincewar kasashe 23 yayin da 14 suka nuna rashin amincewa sannan wasu kasashe 9 suka yi rowar kuri'unsu kuma an ajiye gobe Juma'a don yin muhawara da daukar matakin karshe kan batu.