1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan ya kammala ziyara sa a Siriya

March 11, 2012

Babu wata yarjejeniya da Tsohon sakataran Majalisar Ɗinkin duniya ya cimma da gwamnatin Bashar Al Assad domin dakatar da tashin hankali

https://p.dw.com/p/14J7T
epa03140730 UN Arab League envoy Kofi Annan upon his arrival for a meeting with Syria_s grand Mufti Ahmed Hassoun (not pictured), in Damascus, Syria, 11 March 2012. Annan, who is on a current visit to Syria, held talks with Syrian President Bashar Assad and a number of opposition figures. His call for an immediate cease-fire and political dialogue has been dismissed as a nonstarter by both sides. Assad told Annan on 11 of March that a political solution is impossible as long as 'terrorist groups' threaten the country. Meanwhile, Syrian government troops stormed areas in the restive northern province of Idlib. EPA/YOUSSEF BADAWI
Hoto: picture-alliance/dpa

Manzon na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen larabawa Kofi Annan ya ce ya na da kyaukyawan fatan cewar za a samu masalha a rikicin ƙasar Siriyar ;tsohon babban sakataran na MDD ya baiyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi bayan da ya gana a karo na biyu da shugaba Bashar al Assad.

Wanda ya ce ya gabatar masa da nagartatun shawarwari na samun mafita ;amma du da haka ya ce nauyi da aka ɗora masa na samar da zaman lafiya a Siriya abi ne da ke da wuya.''ya ce a kwai wahala amma ba zamu yanke ƙauna ba, muna sa ran za a cimma nasara ;ya ce kusan dukanin jama'a da na gana da su yan Siriyar a wannan yar guntuar ziyara kowa ne na fatan ganin an sake dawo da zaman lafiya''.Mista Annan ya ce shawarwarin da suka yi da shugaba Assad sun maida hankali ne akan dakatar da tashin hankalin da kisan jama'ar, tare da ba da damar isar da kayan agaji da kuma soma gudanar da tattaunawa da yan adawar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi