1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan ya isa Saudi Arabia

Zainab A MohammedSeptember 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5X

Sakatare general na mdd Kofi Annan,ya isa kasar Saudi Arabia ayau,domin tattaunawa da magabatan wannan kasa ,a rangadin aikin dayake cigaba da yi a yankin gabas ta tsakiya,domin neman goyon bayan kasashen yankin wa kudurin mdd akan Lebanon.A ziyarar daya kai a Qatar tun da farko dai,,Mr Annan yace kamata yayi a warware wannan rikici na Nuclearn Iran ta hanyar suhu.Tun a jiya nedai shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadi nejad,ya fadawa jagoran mdd cewa,Tehran bazata daina bunkasa sinadran uranium dinta ba,amma a shirye take wajen tattauna batun.A hannu guda kuma Kofi Annan ya amince da da shiga tsakani akokarin da ake na sakin sojojin izraela biyu da aka sace,sakamakon rokon da izraela da yan hizbollah sukayi.Izraelan dai ta nemi da sako sojojin nata guda biyu da yan hizbollah suka sace tun ranar 12 ga watan yuli,ba tare gindaya musu kaidoji ba.