Kofi Anan ya gana da shugaban ƙasar Siriya
March 10, 2012Talla
Tsohon babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Anan ya ƙwashe sao'i da dama tare da shi da tawagawar ƙasashen larabawa suna tattaunwa da shugaban na ƙasar Siriya.Tawagar dai ta jaddada buƙutar ganin an kawo ƙarshen tashin hankali da ake fama da shi a siriya wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu biyar.
A hannu ɗaya kuma wasu rahotanin na cewar dakarun gwamnatin na ci gaba da kai farmaki a garin Idelb inda kawo yanzu suka kashe mutane da dama ; wani mazaunin garin ya baiyana abinda ke wakana ''ya ce tun jiya suke yin ruwa wuta ba ƙaƙautawa wanda a ciki kusan mutane 35 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikata.
Mawallafi : Abdourahamane Hasane
Edita : Abdullahi Tanko Bala