1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: 'Yan farar hula cikin gwamnatin soja

August 29, 2024

Kungiyoyin farar hula a Gabon, na shan suka bayan da suka amince da nadin mukaman siyasa a gwamnatin mukin soja karkashin Janar Oligui Nguema da ke cika shekara guda a kan mulki.

https://p.dw.com/p/4k3Wy
Gabon | Sojoji | Janar Brice Oligui Nguema
Jagoran gwamantin sojan kasar Gabon Janar Brice Oligui NguemaHoto: AFP/Getty Images

A yayin da wasu al'ummar ta Gabon ke daukar wannan mataki a matsayin juya baya ga aikin kwato wa al'umma hakki daga hannun masu mulki, wadanda abin ya shafa na cewa wani nau'i ne na gagwarmayar da suka fara na kawar da babakeren iyalin Bongo daga mulkin Gabon kwata-kwata. Shugaban gwamnatin mulkin sojan Gabon din Janar Brice Clotaire Oligui Nguema ya nada wasu jiga-jigan shugabannin kungiyoyin farar hula a cikin gwamnatinsa ne, bayan da ya yi wa Ali Bongo Ondimba juyin mulki. Tun wannan lokaci ne kungiyoyin farar hula suka yi gum da bakinsu, lamarin da ya saba wa tayar da jijiyoyin wuya da suka saba yi domin bayyana matsayi kan wani nau'i na rashin adalcin da al'ummar kasar ke fuskanta. Hasali ma suna neman juya babin gaggwarmaya zuwa fagen siyasa, inda daidai da batun kisan gilla da sojoji suka yi wa fararen hula da neman hakkin wadanda rikicin bayan zaben 2009 da 2016 ya shafa ba ya sha musu kai a yanzu.

Gabon | Sojoji | Juyin Mulki | 2023
Al'ummar Gabon dai, sun yi ta tsallen murna bayan da sojoji suka yi juyin mulkiHoto: AFP/Getty Images

Georges Mpaga da ya himmatu tsawon shekaru wajen kare hakkin dan Adam a Gabon da ke yankin Afirka ta Tsakiya, yana daga cikin wadanda shugaban mulkin sojan ya nada a majalisar kula da tsarin tattalin arziki da zamantakewa da muhallin kasar. Amma dai ya kare matsayinsa yana mai cewa, shigar kungiyoyin farar hula cikin gwamnati abu ne mai fa'ida. A cewarsa dai, kungiyoyin farar hula na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Gabon sau da kafa tare da bayar da shawarwari, sabanin yadda wasu ke tunani kana suna taka tsan-tsan a duk matakan da suke dauka. Wannan karbar mukaman siyasa da kungiyoyin farar hula suka yi a Gabon yana raunana kwarin gwiwar da al'umma ke da shi a gare su, saboda sun lura cewar sun rikide daga muryar talaka zuwa 'yan amshin shata na gwamnatin mulkin sojan Gabon. A zamanin mulkin Ali Bongo Ondimba da aka hambarar dai, kungiyoyin masu zaman kansu na kakkausar suka ga duk wani matakin gwamnati da ya saba da doka da oda da 'yancin fadar albarkacin baki ko kuma ya keta hakkin dan Adam ko tsarin dimukuradiyya.