Juyin mulki da ECOWAS a yammacin Afirka
May 4, 2022Sai dai kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, na shan suka. A yanzu haka dai sojojin sun yi juyin mulki a kasashe uku na yankin yammacin Afirkan, wato a Mali da Guinea da kuma Burkina Faso. Hakan dai ya sa kasashen sun sake dawo da sunan yankin idon duniya saboda rikicin siyasa da ake samu, abin da Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana ya shaidawa majalisar dokokin kasarsa cewa haka abin takaici ne da ke nuna an gaza wajen magance matsalolin siyasa ba tare da sojoji sun tsoma bakinsu har ya kai ga juyin mulki ba. Karkashin jagorancin shugaban na Ghana a kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ne dai, aka samu ECOWAS ta ci gaba da nuna ba sani ba sabo ga wadanda suka yi juyin mulki ta hanyar katse hulda.
Sai dai a cewar Fode Mane na kungiyoyin fararen hula na Guinea Bissau, ba su fahimci inda aka saka gaba ba. Babu wanda ya san abin da ake bukata ko gwamnati ko kuma ECOWAS ko CEDEAO din ke bukata. A cewarsa a Guinea Bissau babu wanda ya yi imanin rundunar tabbatar da zaman lafiya za ta iya magance matsalolin da suke fuskanta. Ya kara da cewa ana ganin rundunar tamkar wata hanya ce ta nuna karfi tsakanin shugabannin manyan kasashen kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO kamar Najeriya da Senegal, inda Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Shugaba Macky Sall na Senegal ke kare abokinsu da sunan kungiyar. Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO dai, na ci gaba da duba dabarun katse hanzarin sojojin da suka yi juyin mulkin.