1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martani kan nasarar yakar cin-hanci

December 9, 2024

Hukumar ICPC da ke yaki da cin-hanci da rashawa a Najeriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce yunkurin da suke na yakar cin hanci da rashawa a cikin kasar ya soma tasiri.

https://p.dw.com/p/4nvuD
Najeriya | Cin-hanci | ICPC | Nasara
An jima ana zargin bayar da na goro a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Tuni dai masana tattalin arzikin kasa da masu fashin baki akan al'amurran yau da kullum a Najeriyar, suka fara tsokaci tare da mayar da martani a kan wannan kididdigar da Hukumar ICPC da ke yaki da cin-hanci da rashawa a kasar ta fitar musamman a yankin Arewa maso Yamma. Tun bayan da shugaban hukumar ta ICPC Dakta Musa Adamu Aliyu ya bayyana cewa kididdigar ta gano cewa kaso 70 cikin 100 na 'yan Najeriya da aka bukaci su bayar da cin-hanci da rashawa a cikin kasar a wannan shekara ta 2024 sun ki bayarwa, sai masana tattalina arziki da masu fashin baki a cikin kasar suka rika  jefa ayar tambaya tare da nu na shakku  ga wadannan kalamai.

Babandede ya yi tir da cin hanci a Najeriya

Tuni dai masu fashin baki da sharhi akan al'amurran yau da kullum a Najeriyar ke bayyana wasu ma'aunai da suke ganin da sune kadai 'yan kasar ke iya yin alkalanci, kafin su iya gamsuwa da irin wannan rahoto na ICPC. Yayin da hukumomi a Najeriya ke cewar an samu raguwar cin-hanci Arewa maso Yammacin kasar, wasu 'yan yankin na cewar an samu karuwar cin-hancin musamman a shingen jami'an tsaro da ke kan tituna. A hannu guda kuma Najeriyar na fuskantar matsin tattalin arziki da galibin talakawan kasar ke koke a kansa, sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi masu bincike a cibiyoyin kudi na bayyana yadda suke kallon wannan kididdigar.