1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kula da 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 28, 2021

Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya bukaci al'ummomin kasa da kasa su kiyaye ka'idojin yarjejeniyar kula da 'yan gudun hijira da aka cimma a Geneva.

https://p.dw.com/p/3yANw
Schweiz Filippo Grandi Flüchtlingskommissar UN
Shugaban Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo GrandiHoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Filippo Grandi ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 70 da cimma wannan yarjejeniya ta Geneva kan 'yan gudun hijirar, inda ya ce ya damu matuka ganin yadda wasu kasashe musamman na Turai ke yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu dangane da batun 'yan gudun hijirar. A cewar Grandi tilas a bi ka'idojin da aka amince da su cikin wannan yarjejniya a duniya baki daya, wajen taimakawa mutanen da ke neman mafaka sakamakon musgunawa da barazana da suke fuskanta a kasashensu na asali. Ya kuma yaba da yarjejeniyar da ya ce, ta taimakawa miliyoyin mutane a duniya.