1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiraye-kirayen kawo karshen yaki a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
July 11, 2023

Kungiyar Human Rights Watch ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ta gudanar da bincike kan laifukan yaki a yankin Darfur, inda ake ci gaba da gwabza fada duk da kiran da ake yi na sasantawa.

https://p.dw.com/p/4TivN
Yadda hayaki ya yurtuke garin Al Fasher na arewacin Darfur sakamakaon yakiHoto: Stringer/IMAGESLIVE via ZUMA Press Wire/picture alliance

Kungiyar HRW da ta himmata wajen kare hakkin bil Adama ta ce a karshen watan mayu kadai, an kashe mutane da dama tare da jikkata dubbai a lokacin da mayakan RSF da kabilun Larabawa suka kai hari a Darfur. Dama dai rahotanni sun nunar da cewa hare-hare ta sama na sake girgiza Khartum babban birnin kasar Sudan.

Sai dai kungiyar Igad ta kasashen gabashin Afrika da Sudan take ciki, ta yi kira da a tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba, a taron wanzar da zaman lafiya da ke gudana a Addis Ababa. Amma masana tsaro na ganin cewar jagororin yakin Janar al-Burhane da Janar Hamdane Daglo sun zabi neman nasara ta hanyar yaki maimakon tattaunawa don samar da masalaha.