1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tasirin takunkuman Rasha ga kasashen Larabawa

Mahmud Yaya Azare AMA
February 25, 2022

A yayin da Rasha ke fuskantar jerin takunkumai daga manyan kasashen duniya, masharhanta na tsokaci kan tasirin da hakan zai yi ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya abokan huldar Rasha.

https://p.dw.com/p/47d7j
Ukraine-Konflikt - Tag des Verteidigers des Vaterlandes
Hoto: Alexei Nikolsky/Sputnik Kremlin/AP/dpa/picture alliance

Kasar Siriya da ke da sansanin sojin Rasha mafi girma a gabar Teku na kan gaba daga kasashen da ake ganin takunkumin da kasashen Yamma ke ta rige-rigen kakaba wa Rasha zai yi matukar tasiri, kasancewarta tana dogaro ne kacokam da kasar Rasha wajen tsaronta da ma aiwatar da kwangilolin sa ke gina kasar da tallafa wa tattalin arzikinta da yakin basasar shekaru goma ya durkusar.

Karin Bayani: Rudani bayan fara yakin Rasha da Ukraine 

Dr Ibrahim Nafisy, wani mai fashin baki kan alakar Rasha da kasashen Larabawa ne kuma duk da ya tabbatar da cewa "Takunkuman da ake kakaba wa Rasha zai yi mummunan tasiri ga kasar Siriya da ma kawayen Rasha a yankin.Sai dai Dr Ibrahim  Nafisy ya yi arashin cewa kasar Rasha za tai iya kokarinta wajen ganin ta huce haushinta ko rage asara kan yan kazaginta a yana mai cewa."Shelar da Shugaba Vladimir Putin ya yi dangane da aniyarsa ta shiga yakin na "sai baba ta gani" don kare muradan Rasha na ketare, sako ne ga duniya kan cewa ba zai taba yin watsi da kasashen da yake kawance da su ba a halin yaki ko zaman lafiya, ciki har da kasar Siriya da ke zama babbar sansanin sojinsa a yankin Gabas Ta Tsakiya." 

Karin Bayani: Hankula sun koma kan Rasha da Ukraine

To sai dai a sabanin wannan hasashen Dr Abdussalam Aqal wani masanin tattalin arziki a lokacin yaki na ganin cewa koda takunkumin bai yi nasarar durkusar da tattalin arzikin Rasha da kawayenta a yankin ba, zai rage irin karfin fada ajin da suke da shi a yankin, yana mai cewa."Abun da zai kara dagula lamura ga kawayen Rasha yankin shi ne kawancen NATO da ke dagewa wajan kakaba wa Rasha takunkumi mai tsanani bayan sayar wa shuwagabanin yankin makaman da Rasha ke iya sayar masu. Idan kuma har kasashen suka fara aiki da takunkumin  hana Rasha amfana da tsarin aikawa da kudade na kasa da kasa mai suna SWIFT, to hakan zai kawo karshen cinikin makaman da Saudiyya da Iran ke yi da Rasha, lamarin da zai iya jawo raguwar tura muggan miyagun makamai da Iran da Rasha ke yi zuwa Yemen, ya kuma tilasta wa Rasha janye sojojin hayarta na Wagna a Libiya."Rasha da Ukiraine suke sayarwa kasashen Larabawa da kaso 70 cikin dari na alkamar da suke ci.