1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kimamin ´yan yawon bude ido 20 aka yi garkuwa da su a Ethiopia

March 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuQm

Hukumomi a kasar Ethiopia sun ce sun yi imani baki kimanin 20 ne aka yi garkuwa da su a wani yankin karkara na kasar inda ´yan tawaye suka kafa sansani. Tun a ranar laraba ´yan yawon bude ido da suka hada da ´yan kasar Faransa 10 da kuma wasu mutane 10 daga kasashe dabam dabam suka bata a lokacin da suke ziyartar yankin Afar dake can arewa maso gabashin Ethiopia. Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margaret Beckett ta tabbatar da cewa ma´aikata biyar na ofishin jakadancin Birtaniya a Addis Ababa na daga cikin mutanen da suka bata. A cikin shekarun baya-bayan nan yankin na Afar ya kasance wata cibiyar garkuwa da ´yan yawon bude ido.