1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiir da Machar ne shirin kafa gwamnati

Mouhamadou Awal Balarabe
December 17, 2019

Shugaba Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan ta Kudu kafin karshen watan fabreru.

https://p.dw.com/p/3Uxfq
Südsudan Juba - Riek Machar, Salva Kiir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Patinkin

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun sha alwashin mutunta wa'adin kwanaki 100 da suka diba don kafa gwamnatin hadin kan kasa. Bayan wata ganawa da bangarorin biyu suka yi a wannan Talata, shugaban kiir ya ce sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa kafin karshen watan fabrairu mai zuwa. Sai dai kuma a nasa bangare Riek Machar ya ce har yanzu ba su warware matsalar yawan jihohi da ya kamata Sudan ta Kudu ta kunsa ba.

Kasashen duniya sun jima suna nuna damuwa kan rikicin shugabanci da jaririyar kasar Sudan ta Kudu ta shafe shekaru tana fama da shi. An dai taba kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin Salva Kiir da Riek Machar, amma kuma ba ta dore ba sakamakon sabanin da ke tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.