Birnin Kherson ya koma hannun Ukraine
November 12, 2022Talla
Wasu kasashe aminan Ukraine na cigaba da aika sakon taya kasar murnar karbe iko da yankin Kherson na kudancin kasar daga Rasha, makwanni bayan da ta ayyana shi a daya daga cikin yankunanta.
Amirka ta bayyana nasarar a matsayin gagaruma a yayin da Faransa ta ce ta yi farin cikin ganin yankin ya koma karkashin Ukraine.
Shugaba Zelensky, ya bayyana nasarar a matsayin irinta ta tarihi da sojojin kasar suka yi, tare da cewa yanzu sojan kasar ne ke sintirin don tabbatar da doka da oda.
A sakon da ya bayyana a wannan Asabar ministan harkokin wajen Uklraine Dmytro Kouleba, ya ce za a ci gaba da fafatawa sannan kasar na da bukatar ci gaba da samun tallafin aminanta.