1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: 'Yan sanda sun kashe gomman mutane a 2023

April 24, 2024

Kungiyoyin kare hakkin bil Adam na Kenya da kuma na kasa da kasa sun ce 'yan sanda sun kashe mutane ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/4f8rL
Hoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Kungiyoyin da suka hada da Human Rights Watch da Amnesty International da kuma Kenya group Missing voices sun ce rabin kashe-kashe an aikata su ne a lokacin da ake gudanar da ayyukan yaki da miyagun laifuka.

Yayin da sauran mutane 45 an kashe su ne a lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar da aka gudanar a tsakanin watannin Maris da kuma Juli na shekarar 2023.

Karin bayani:Kenya: An zargi 'yan sanda da kisan mutane

Rahoton kungiyoyin ya kuma ce, ba kasafai ake kama 'yan sandan suka aikata kisan gilla da kuma hannu wajen batar mutane. Sai dai kuma Kakakin rundunar 'yan sandan Kenya, Resila Onyango bata mayar da martani kan lamarin ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun sha zargin jami'an 'yan sandan Kenya da amfani da karfin tuwo kan jama'a mussaman a unguwannin 'yan rabbana ka wadata mu, sai dai kuma gwamnatin kasar ta dade ta na cewa tana daukar mataki.