1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta yi gargadi kan rikicin Sudan ta Kudu

April 26, 2014

Shugaban Kenya ya ce ba zai amince da kisan kare dangi a Sudan ta Kudu ba. Sai dai kuma bai bayyana hanyoyin kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi ba

https://p.dw.com/p/1Bosg
Hoto: AFP/Getty Images

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ba zai hade hannu ya bar rikicin kasar Sudan ta Kudu ya zama kisan kare dangi ba. A cikin wata sanarwa shugaban ya ce yankin ya yi watsi da yiwuwar samun kisan kare dangi. Amma sanarwar ba ta fito fili ta yi karin haske kan matakan da shugaban ya ke neman dauka ba, bisa abin da ke faruwa a kasar ta Sudan ta Kudu.

Daya daga cikin makwabta kasar wato Uganda ta tura dakaru zuwa Sudan ta Kudu, wacce ta fadacikin rikicitun watanni hudu da suka gabata, lokacin da Shugaba Salva Kiir ya yi zargin cewa tsohon mataimakinsa Riek Machar ya nemi kifar da gwamnatinsa, abin da ya jefa kasar cikin rikici mai nasaba da kabilanci, tsakanin kabilun mutanen biyu. Majaliasar Dinkin Duniya ta yi zargin cewa an aiwatar da kisan kare dangi mai nasaba da kabilanci a Sudan ta Kudu, kuma ta bayar da umurnin aiwatar da bincike.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe