1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen ayyukan rundunar MONISCO a Kwango

Binta Aliyu Zurmi
August 12, 2023

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar ayyukan Majalisar a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango ya shiga sahu na karshe.

https://p.dw.com/p/4V5dL
USA UN-Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Ed Jones/AFP

A wani rahoto da ya gabatarwa kwamitin sulhu na MDD, Guterres ya  bayyana shirin da ma tsare-tsaren janye rundunar MONUSCO bayan kwashe kusan shekaru 25 tana aiki a kasar.

Rahoton mai shafuka 15 ya nuna yadda cin zarafin mata da kananan yara ya rubanya daga shekarar 2021 zuwa 2022.

Kazalika ya yi gargadin lamuran tsaro a kasar da ta jima tana fama da rikici na ci gaba da tabarbarewa.

Yankin kudancin Kivu da Ituri na daga cikin yankunan da lamarin ya fi kamari, inda sama da kaso 28 zuwa 39 na al'ummar yankin rikici ya raba su da matsugunnansu.