1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240412 Hannover Messe Deutschland China

Zainab MohammedApril 25, 2012

Kamfanonin kere-kere anan tarayyar Jamus na fuskantar babbar kalubale na gasa a kasuwannin duniya, inda har masana'antun China dake tasowa, za su iya kasancewa babbar barazana.

https://p.dw.com/p/14kc0
Bundeskanzlerin Angela Merkel und der chinesische Premierminister Wen Jiabao beim Messerundgang vor einem Modell der Baiyun Power Group. Die Energiefirma aus Guangzhou im Süden Chinas präsentiert ihre Zentrale als grünes Vorzeigeprojekt, das erneuerbare Energien zu einem intelligenten Netz verbindet. Allerdings liegen Wunsch und Wirklichkeit noch weit auseinander. Foto DW/Per Henriksen 23.04.2012. DW1_9545.jpg
Hoto: DW

Waɗanne irin matakai ya dace kamfanonin Jamus din su ɗauka, domin su cigaba da rike martabarsu da aka sansu dashi na sarrafa ingantattun kaya? Mahalarta taron baje kolin kayayyakin masana'antu mafi girma da ke gudana a birnin Hannover sun bayyana ra'ayoyinsu. Baje kolin da China ta kasance abokiyar haɗin gwiwar Jamus wajen shiryawa.

Yawancin kamfanonin Jamus dai a rayuwarsu na fuskantar matsin lambar sarrafa ingantattun kayayyaki ne, domin fitar wa zuwa kasuwannin duniya. Abunda ya kasance sabo a yau, zai iya kasancewa matsayin da ake bukatar kowa ya cimma a gobe. Abunda kawai zai ɗore kuma ya dawwama shine sabbin fasahar ƙirƙira da basira, a cewar Thomas Lindner shugaban kungiyar masana'antu ta VDMA:

" Musamman saboda hajojinmu da zamu fitar zuwa kasuwannin duniya, ya zamanto wajibi mu tursasa matakan da suka dace wajen fasahar kirkiro ingantattun kayayyaki, wanda ingancin ne zai kare martabar waɗannan fasahu namu a gaban saura makamantansu".

To sai dai ayar tambaya anan ita ce, har zuwa wane tsawon lokaci za'a dogara da hakan. Idan za'a cewa mutuminda ke sauri, bashi da wani zabi sai kara gudu. Amma acewar Liu Hong yanayin yayi sauki. Kwararren da ayanzu Farfesa ne a cibiyar nazarin fasaha ta Harbin ya yi shekaru 20 a nan tarayyar Jamus:

" Na yi imanin cewar , Jamus tana rukuni na gaba idan ana maganar ingancin kaya, ayayinda China take da matsakaita zuwa kananan masana'antun gine-gine".

Bukatar sarrafa kaya masu inganci

Shima Ralf Hausmann na kamfanin sarrafa kayyakin wutar lantarki na Poenix dake nan Jamus yayi imani da hakan....

" Zan faɗa ba tare da wata tantama ba cewar, kayayyakin da muke sarrafawa anan Jamus shine kan gaba a inganci, idan ana kwatantawa da kamfanonin China. Wannan shi ne nawa ra'ayin. Domin na sani muna da alkawari a gabatar da ingantattun kaya".

Ralf Hausmann dai yayi imanin cewar, ci gaban kowace fasaha dama basirar ƙirƙirar sabbin hajoji, ya ta'allaka ne a banganren masu masana'nsu su saurari matsalolin masu cinikinsu.

" Yace basirar kirkirar sabon abu na nufin, sarrafa hajojin sa suke tserewa na sauran abokan gasarka ta ko wace siga. Kuma wadanda mabukatu abokan cinikinka zasu iya amfani dashi. Kana su yi alfaharin cewar wannan kaya yana da inganci, gashi da takaita lokaci da farashi mai madaidaici, waɗannan sune irin kayyaki da muke sarrafawa ".

Kamfanin sarrafa kayan hutan lantarki na Phoenix Contact mai matsuguni a kusa da birnin Bielefeld dake jihar Nordrhei-Westfalen dake nan jamus, dai na da ma'aikata wajen dubu 12, kuma yayi fice a samarda ingantattun kayayykin amfanin lantarki. A yanzu haka wannan masana'anta ta na aiki a kasar China, saboda sanin muhimmancin hulda ta kai tsaye da mabukatunta.

Sayen Na gari mai da kuɗi gida

Hakan dai ya kasance ra'ayin kananan kamfanoni kamar LTG AG mai sarrafa fankar samar da iska da abun tace ruwa dake birnin Stuttgart mai ma'aikata 150. A cewar Michael Lipowitch na wannan masana'anta, suna sarrafa ingantattun fanka, kana su tsabtace kewayensu ta hanyar kwashe dukkannin karafa da suka yi amfani dashi, domin sake sarrafa shi zuwa wani salon. Yace ko shakka babu akwai kamfanonin China dake sarrafa na'urorin sanyaya wuri kamar fanka, wadanda kuma suke da saukin farashi, sai ko kadan ba za'a iya kwatanta ingancin su da kayayyakin da kampaninsa ke sarrafawa ba, wadanda kan ziyarci inda masu cinikinsu suke domin suyi nazarin irin na'urar da ake bukata domin ko wane irin amfani.

Wani abun da ke da muhimmanci inji mahalarta wannan baje koli na kayayyakin masana'antu shine, yin fice a dukkan irin kayyakain da kake sarrafawa, tare da zama cikin shirin rungumar kowane sauyi na zamani ya bayyana dangane da irin hajojinka.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe