1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Rabin al'umma sun yi riga-kafin corona

Binta Aliyu Zurmi
August 31, 2021

Shugabar Hukumar Gudanarwa ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, an yi wa sama da kaso 70 cikin 100 na al'ummar nahiyar da suka haura shekaru 18 allurar ri-gakafin corona.

https://p.dw.com/p/3zjej
Spanien | Ursula Von der Leyen besucht ein Aufnahmelager für Evakuierte aus Afghanistan
Hoto: Juan Medina/REUTERS

Wannan dai shi ne burin da kasashe mambobinn kungiyar ta Tarayyar Turai wato EU suka sanya a gaba tun a farkon wannan shekarar, inda suke fatan ganin ya zuwa yanzu sama da rabin alu'umma sun yi alurar.

A wani sakon bidiyo da ta wallafa a kafar internet, von der Leyen ta ce: "Mun cimma burinmu da ke da matukar muhimmanci a yaki da wannan cuta ta coronavirus, kaso 70 cikin 100 na alummarmu na da cikakkiyar kariya. Hakan na nufin sama da mutum miliyan 250, sun yi allurarsu duka."

Bullar nau'in Delta na zama babban kalubalen da duniya ke fuskanta a yanzu haka, lamarin da ya kai ga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta nuna damuwa ga irin yawan wadanda cutar za ta halaka nan da zuwa karshen wannan shekara ta 2021 da muke ciki.