1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashoggi ya nuna damuwa gabanin kisansa

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 26, 2018

Budurwar shararren dan jaridar nan dan asalin kasar Saudiyya da aka yi wa kisan gilla a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan a birnin Santabul na Turkiyya Jamal Khashoggi ta ce bai so zuwansa ofishin ba.

https://p.dw.com/p/37GJk
Hatice Cengiz verlobte des ermordeten Jamal Khashoggi im TV Interview
Hatice Cengiz budurwar Jamal KashoggiHoto: Reuters/Haberturk

A hirarata ta farko da wani gidan talabijin din Turkiyyan cikin wani shiri mai suna Haberturk, budurwar Kashoggi mai suna Hatice Cengiz ta bayyana cewa ba za a ce Khashoggi yana fargabar za su iya hallaka shi bane, sai dai yana tunanin za su yi masa zafafan tambayoyi ko kuma su tilasta mishi komawa Saudiyyan. Cengiz ta kara da cewa:

"Bamu yi wata doguwar tattaunawa da shi kan batun ba, sai dai na tambaye shi: Me yasa baya son zuwa? Ya damu matuka, ina iya karantar hakan daga idanunsa."