EU ta nemi a aiwatar da sauyi a Hukumar Lafiya ta Duniya
October 30, 2020Kasashen Turai sun nemi a bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) karfin ikon da zai bata damar tunkar duk wata annoba. Akwai bukatar a aiwatar da sauye-sauye a tsarin aikun hukumar ta la'akari da tarin matsalolin da ta fuskanta da ya kuma fito da gazawarta a yayin bullar annobar corona.
WHO ta sha suka bisa kin daukar mataki a kan lokacin domin hana yaduwar cutar da yanzu haka ta kama mutum fiye da miliyan arba'ain. Hukumar Lafiya na bukatar gudanar da aikin tattara bayanai na alkaluman wadanda suka kamu da cuta da zarar an sami bullarta ba tare da sai ta jira alkaluman da kasashe za su bata ba, wannan ake ganin zai taimaka a shawo kan annobar kafin ta yi illa.
Kasar Chaina inda corona ta samo asali, na daga cikin kasashen da aka zargi mahukuntan da yin rufa-rufa kan girman cutar da ta addabi duniya. A wata mai zuwa ake son zama da hukumar don nazari a game da sauye-sauyen da zai bata damar daukar matakin shawo kan annoba cikin gaggawa ba tare da jiran amincewar kasa ba.