1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a bude iyakokin cikin gida na Turai

Binta Aliyu Zurmi MNA
June 15, 2020

A yayin da kasashen nahiyar Turai ke shirin bude iyakokinsu daga wannan rana ta Litinin 15 ga wata Yuni watanni bayan rufe su, kasashe da dama na ta shirye-shiryen karbar baki masu yawon bude ido.

https://p.dw.com/p/3dlvX
Brüssel EU Coronavirus Luftbrücke Demokratische Republik Kongo
Hoto: picture-alliance/abaca/M. Thierry

A wannan Litinin da yawa daga cikin kasashen Turai na kungiyar EU ke bude kan iyakokinsu watanni da dama bayan rufe su saboda cutar COVID-19.

Sai dai akwai bukatar ko da an bude iyakokin mutane kar su yi nisa da kasashensu a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasashen musamman a fannin yawon bude ido.

Faransa da ke zama kasa ta farko a wannan fanni na kira ga al'ummar ta da su yi hutunsu na rani a cikin kasar maimakon kai kudadensu wasu kasashen. A yayin da a hannu guda suke shirin fara wani shiri mai taken "A Faransa zan yi hutun rani na"

Kasar Spain ta sanar da cewar ba za ta bude iyakokinta a wannan rana ba a yayin da ta ke shirin karshe na karkabe cutar COVID-19. Birtaniya wacce dama bata rufe nata iyakokin ba bata cikin wannan shirin sai dai ta ce duk mai shiga kasarta sai ya yi makwanni biyu a kebe.