1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Koriya sun dauki aniyar kawo canji

Zulaiha Abubakar
September 19, 2018

Kasar Koriya ta Arewa ta amince zata lalata wata cibiyar makaman Nukilar ta a gaban masana makami daga kasashen ketare tare kuma da daukar alwashin rufe babbar cibiyar makaman bisa sharadi tsakanin ta da Amirka.

https://p.dw.com/p/357sc
Innerkoreanischer Gipfel
Hoto: Korea Summit

Shugaba Kim Jung Un na Koriya ta Arewa da takwaransa Moon Jae-In na Koriya ta Kudu sun bayyana cewa sun shirya tsaf don mayar da yankin na Koriya sansanin zaman lafiya da yanci ba tare da fargabar harin kare dangi ba. Da yake tofa albarkacin bakin sa game da wannan sabon cigaba Shugaba Donald Trump na kasar Amirka ya bayyana matsayar da abin a yaba.