1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara rigakafin Corona

December 27, 2020

Mutane sama da miliyan dari hudu da hamsin ne za a yi wa rigakafin Corona a kasashen kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/3nGB4
Rotterdam | Impfstoff Zulassung | Pfizer und BioNTech
Hoto: Robbin Utrecht/picture alliance

Kasashe ashirin da bakwai na kungiyar Tarayyar Turai ta EU sun kaddamar da fara allurar rigakafin Corona a wannan  Lahadi a kasashensu, biyo bayan kammala rarraba alluran a ranar Asabar.

Shugabar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen ta ce kimanin mazauna kasashen EU dubu hudu da hamsin ne ake sa ran yi wa rigakafin cikin 'yan watanni. Tuni dai kasashen suka bude cibiyoyin bayar da rigakafin.

Da ma can wasu daga cikin kasashen sun fara wannan aikin tun a ranar Asabar, da suka hada da Hungary da Slovakiya da Jamus da dai sauransu.