1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya za su talllafawa Sudan

June 19, 2023

Kasashen duniya masu bada agaji sun sha alwashin bayar da tallafin dala biliyan daya da rabi ga Sudan da kuma kasashen da suka makwaftaka da ita.

https://p.dw.com/p/4SmsN
Haiti Geberkonfernz
Hoto: AP

Hakan dai na zuwa ne bayan kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na kara yawan tallafi ga kasar da ke fama da rikici wanda ya tilastawa mutane fiye da miliyan biyu rasa matsagunnansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kasar na bukatar agajin dala biliyan uku a wannan shekarar domin gudanar da ayyukan jin kai dama tallafawa 'yan gudun hijira, wanda kawo yanzu aka samu rabin kudin.

Jamus ta ce za ta bada tallafin dala miliyan dari biyu da 18 yayin da Amirka ta ce nata gudunmawar zai kasance dala miliyan 171, ko baya ga MDD da ta ce za ta bayar da karin dala miliyan 22. Fada dai tsakanin bangaran dakarun sojin kasar da kuma na kungiyar RSF na kara kazanta, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 3.