1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya za su karfafa tsaro a Somaliya

Usman ShehuFebruary 22, 2012

A wani matakin tabbatar da tsaro ya inganta a kasar Somaliya, a yau Majalisar Dinkin Duniya za ta yi kuri'ar kara dakarun kiyaye zaman lafiya

https://p.dw.com/p/147MK
Hundreds of newly trained Shabaab fighters perform military exercises in the Lafofe area some 18Km south of Mogadishu on Thursday Feb. 17, 2011. In information which could not be independently verified, Islamist officials who spoke during the show of the force, said that five hundred fresh fighters have participated in the training session which was concluded recently and will be part of the war against Somalia government and the African peacekeepers supporting them.(AP Photo/Farah Abdi Warsameh) Für Projekt Destination Europe Mangelnde Perspektiven und große Träume
Gründe für Migration Krieg Somalia Muslime ethnische Konflikte VerteibungHoto: AP

A yau ne MDD za ta kada kuri'ar domin kara yawan dakarun kiyaye zaman lafiya a kasar Somaliya. Kungiyar Tarayyar Afirka wanda kawo yanzu dakarunta ne ke wanzar da zaman lafiya a Somaliya, tana bukatar a kara yawan dakarun daga 12000 izuwa dubu goma 17000. A barane dai dakarun kasashen Afirka dake Somaliya suka samu nasarar fatattakar mayakan Alshabab a aksarin babban birnin kasar da kuma wasu wurare dake kusa da birnin na Mogadishu. Batun kada kuri'ar da MDD za'a yi shine kwana guda kafin taron da kasashen duniya za su yi kan kasar ta Somaliya a birnin london. Manufar taron shine a kara shirin marawa gwamnatin rikon kwaryan kasar da a yanzu bata da cikkaken iko. Shugaban hukumar Tarayyar Turai wanda kuma itace tafi baiwa Somaliya tallafi mai soka, ya yi alkawarin cewa EU za ta kara agajin da take baiwa Somaliya. A halinda ake ciki kungiyar kare hakkin bil'adama ta HRW ta zargi zagerun Alshabab da yin amfani da yara kanana a matsayin soja.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu