1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe na son a kwato wa Musulmin China hakki

November 1, 2022

Kasashe 50 galibi na yammacin duniya, sun bukaci China da ta aiwatar da shawarwarin da Majalisar Dinkin Duniya kan take hakkin Musulmi 'yan kabilar Uyghur.

https://p.dw.com/p/4IvY9
Musulmi 'yan kabilar Uyghur a yankin Xinjiang na China
Hoto: Getty Images

Cikin wata sanarwar da kasashen da galibin su na yammacin duniya ne suka sanya wa hannu, su bayyana yadda suka damu da irin yadda suka gano ake cin zarafin bil Adama a yankin Xinjiang da ke a China inda Musulmi 'yan tsiraru ke ciki.

Daga cikin shawarwarin da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar kan batun dai, har da bukatar gaggauta sakin duk wasu Musulman 'yan kabilar Uyghur da China ke tsare da su ba bisa hakki ba.

Sanarwar wacce aka karanta a zauren Majalisar Dinkin Duniya, na bukatar majalisar, ta bukaci da a dauki matakan da suka dace wajen ganin an taka wa China burki a game da gallazawar da take yi wa tsirarun Musulmin a kasar.

Sai dai kuma gwamnatin China na musanta zargin, tare da yin watsi da duk wani rahoto da ke nuna cewa ana cin zarafin 'yan kabilar ta Uyghurs.

Kasashen dai da ke wannan kira sun hada da Amurka da Japan da Faransa da Jamus da Australia da Isra'ila da Turkiyya da Guatemala har ma da Somaliya.