1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farashin fetur na barazana ga kasar Rasha

March 18, 2020

Ministan kudi na Rasha Anton Siluanov ya sanar wa kamfanin dillancin labarai na Jamus, DPA, cewa kasarsa na fuskantar gibin kusan dalar Amirka bilyan 40 a kasafin kudinta.

https://p.dw.com/p/3Ze0D
Russland Moskau Präsident Putin im Parlament
Hoto: Reuters/Sputnik/Kremlin/A. Nikolsky

Lamarin dai ya jefa kasafin kudin kasar Rasha cikin mawuyacin hali. Ministan kudi na Rasha Anton Siluanov ya ce faduwar farashin man fetur ce ta jefa kasar cikin wannan kangi.

Sai dai kuma ministan ya ce kasar tana da abin dogaro.

''Muna da kudi da muka tanada domin irin wannan rana, akwai asusu na musamman da muka sanya masa kudi don rage radadin da tattalin arzikinmu ka iya fuskanta''

Farashin man fetur da ke zaman daya daga cikin jiga-jigan tattalin arzikin kasar Rasha ya fadi har sau uku tun daga farkon wannan wata na Maris. Masana kuma sun dora alhakin wannan hali da gazawar kungiyar OPEC mai sa ido kan sayar da fetur a kasashen duniya, ta kasa takaita yawan adadin fetur din da kasashen duniya ya kamata su rinka fitarwa a daidai lokacin da farashin fetur din ya fadi warwas a kasuwannin duniya.