1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasa ta rufta da mahaka tagulla

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2023

Ma'aikatan ceto na ci gaba da neman a kalla masu hakar ma'adinai 25 da suka makale a karakshin kasa sakamakon zabtarewar laka a wata budaddiyar ma'adinan tagulla.

https://p.dw.com/p/4ZoM8
Wasu masu hako ma'adinai a bakin aikiHoto: LUIS TATO/AFP

Ma'aikatan da ke aiki a wani wurin hakar ma'adinan na 'Seseli' da ke Chingola mai tazarar kilomita 400 daga arewa maso yammacin Lusaka babban birnin kasar Zambiya, sun makale a wurare uku a daren ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2023.

Bayanai na cewa ana fuskantar cikas a ayyukan ceton sakamakon ruwan sama mai karfi da ya mamaye ramukan da suka zabtare da ma'aika a ciki.

Jami'an gwamnatin kasar sun ce sama da masu hakar ma'adinai 30 ne ke makale a karkashin laka, sai dai babu tabbacin adadin mutanen da lamarin ya ritsa da su. 'Yan sanda sun ce ana zargin dukkan mahaka ma'adinan sun mutu kuma sunayen bakwai daga cikinsu kamar yadda aka tabbatar da mutuwarsu.