1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar kin jinin 'yan Isra'ila da addini Islama

Binta Aliyu Zurmi
November 4, 2023

Shugaban Hukumar Kula da Kare Hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya yi tir da karuwar kin jinin 'yan Isra'ila da ma addinin Islama da ake gani a 'yan kwanakin nan.

https://p.dw.com/p/4YP0n
Schweiz, Genf: Volker Türk, UN-Hochkommissar für Menschenrechte
Hoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/dpa/picture alliance

Mr. Turk ya ce tun bayan harin ranar 7 ga watan jiya da kungiyar Hamas ta kai Isra'ila, ake ganin munanan kalaman tsana a shafukan sada zumunta da ma a tsakanin al'umma a bangarori daban-daban na duniya, abin tir ne da Allah wadai.

Kazalika shugaban na Hukumar kare hakkin Bil Adama ya ce Musulmai da 'yan Isra'ila na bayyana yadda rayukansu ke a cikin hadari, lamarin da ke tayar da hankali.

Ya kuma yi tsokaci a kan yadda kasashen duniya musamman na yammaci ke murkushe masu zanga-zangar adawa, inda ya ce hakan take hakki ne na al'umma.

An shiga mako na 5 ke nan tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya a kan Hamas biyo bayan harin da ta kai mata da ya hallaka Isra'ilawa 1,400, sama da Falasdinawa dubu 9500 ne ya zuwa yanzu ma'aikatar lafiyar Hamas ta tabbatar da mutuwarsu.

 

karin bayani: Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce adadin Falasdinawan da hare-haren Isra'ila suka hallaka ya haura dubu tara