1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen zaman dirshan a birnin Kiev

February 16, 2014

Masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a kasar Ukraine sun kammala ficewa daga dandalin neman 'yanci na Kiev babban birnin kasar da suka mamaye.

https://p.dw.com/p/1BA0H
Hoto: DW/O. Sawytsky

Masu zanga-zangar da suka shafe watanni uku suna zaman dirshan a dandalin neman 'yancin na Kiev babban birnin kasar sun fice daga dandalin ne bisa alkawarin da suka dauka na musayar barin gurin da sakin baki dayan masu zanga-zangar da gwamnati ta cafke.

A yau ne dai masu fafutukar dake zanga-zangar kin jinin gwamnati a Ukraine din suka kammala ficewa daga dandalin 'yancin na Kiev bayan da gwamnati ta saki baki dayan masu zanga-zangar da jami'an tsaro suka kama har su 234.

Rikicin na Ukraine dai ya samo asali ne tun bayan da Shugaba Viktor Yanukovych na kasar ya zabi inganta dangantakarsa da kasar Rasha maimakon karfafa alaka da Tarayyar Turai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba