1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe taron 'yan jarida na duniya

June 18, 2024

An kawo karshen taron kwanaki biyu na 'yan jarida na kasa da kasa da tashar DW take shiryawa duk shekara. A wannan shekarar taron ya mayar da hankali ne kan musayar ra'ayoyi domin samun mafita ga matsalolin aikin jarida.

https://p.dw.com/p/4hDNq
GMF 2024 | Taron 'yan jarida
Taron 'yan jarida na GMFHoto: Ayse Tasci/DW

Batutuwan kare 'yancin dimokradiyya da na fadin albarkacin baki da kuma na 'yan jarida na daga cikin batutuwan da suka mamaye taron. A rana ta biyun na taron an tabo batutuwa da dama da suka shafi nahiyar Afirka da ma yadda sauyin yanayi ke mummunan tasiri a nahiyar, ko baya ga batun rikice-rikice da yankin Sahel ke ciki da kuma matsalolin tsaro da suka yi wa yankin dabaibayi. A lokacin da yake tsokaci dangane da taron, dan jarida kuma masanin Sadiq Abba, ya ce idan aka yi la'akari da taken taron, amfani da karfi ko tsinin bindiga ba shi ne mafita ba wajen kawo karshen matsalolin yankin Sahel da ke barazanar fadawa cikin kangin yunwa. 

GMF 2024 | Taron 'yan jarida
Taron 'yan jarida na GMFHoto: Björn Kietzmann/DW

Batun sauya labaran da ake yadawa a kan nahiyar Afirka na daga cikin abubuwan da ya dauki hankali a taron. An kuma tabo batun makomar aikin jarida a nan gaba, yayin da kirkirarriyar fasaha ta AI ke ci gaba da yin tasiri cikin sauri a rayuwar jama'a har ma da fannin jaridar. 'Yan jarida daga sassa daban-daban sun bayyana yadda wannan fasaha ta AI za ta saukaka aiki da a wasu lokutan ke da matukar wuya da cin lokaci.

An kuma tabo batun karfafawa matasa da ke da muradin shiga aikin jarida a nan gaba duk da cewa suna ganin yadda wasu 'yan jaridan ke rasa rayukansu yayin da wasu ake tsare da su a gidajen yari, a gefe guda kuma a wasu kasashen matasan na rayuwa ne a inda ake take hakkinsu.