1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen taron Majalisar Dokokin China

March 14, 2012

Bayan kwanaki goma na mahawara 'yan Majalisar Dokokin China sun rattaba hannu kan mahimman kudurori

https://p.dw.com/p/14KFO
National Peoples Congress in Beijings Great Hall of the People.jpg Chinese President Hu Jintao delivers a speech at the closing ceremony of the National People's Congress in Beijing's Great Hall of the People Tuesday, March 18, 2007. The annual session of China's ceremonial parliament was drawing to a close Tuesday, overshadowed by deadly anti-government protests in Tibet. (AP Photo/Oded Balilty)
Hoto: AP

Bayan kwanaki goma na mahawarori,Majalisar Dokokin kasar China ta kammalla taronta na shekara.

Wasu daga mahimman kudurorin da 'yan Majalisar suka rattabawa hannu, sun hada da kasafin kudin shekara 2012, da kuma wata ayar doka, wadda ake ta kai ruwa rana kanta, wadda ta ba jami'an tsaro damar daure mutum a sirrance.Duk da adawar da wannan doka ta ci karo da ita daga kungiyoyin kare hakkokin bana adama na kasa da kasa, kashi 92 cikin dari na 'yan majalisar China suka amince da ita.

Wannan shine babban taron karshe na Majalisar China, kamin girka gwamnatin rikwan kwarya a karshen wannan shekara.

A jawabinsa na rufe taro Firaminista Wen Jia Bao, ya nuna goyan baya ga bukatar kasashen larabawa ta girka demokradiya, saidai a fakaice ya jaddada goyan bayan China ga gwamnatin Siriya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu