1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO startet Raketenschutzschild

May 21, 2012

Ƙungiyar NATO ta sanar da fara yin aiki da na'urar bada kariya daga hare haren makamai masu linzami ga ƙasashen Turai na wucin gadi.

https://p.dw.com/p/14zKT
NATO Secretary General Anders Fogh Rasmussen holds a news conference at the Alliance headquarters in Brussels April 18, 2012. NATO foreign and defence ministers will refine plans for withdrawing combat troops from Afghanistan this week in a meeting that comes after an insurgent attack in the heart of Kabul and recrimination from the alliance's Afghan allies. REUTERS/Yves Herman (BELGIUM - Tags: MILITARY POLITICS CONFLICT)
Sakatare janar na ƙungiyar NATO Anders Fogh RasmussenHoto: Reuters

Shugabannin ƙungiyar ƙawacen tsaron NATO mai ƙasashe mambobi 28 dake halartar babban taron da birnin Chicago na ƙasar Amirka ke karɓar baƙunci, suka ce ƙaddamar da fara aiki na wucin gadin, shi ne mataki na farko a burin da ƙungiyar ta sanya a gaba na kammala samar da na'urar kariyar nan da shekara ta 2020, kamar yanda sakatare janar na ƙungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen yayi ƙarin haske:

" Ya ce, wannan shi ne mataki na farko na cimma manufar da muka sanya a gaba na dogon lokaci na samar da cikakkiyar kariya ga ɗaukacin al'ummomin ƙasashen Turai dake da wakilci a cikin ƙugiyar ƙawancen tsaron NATO tare da yankuna da kuma dakarun su."

Sabuwar na'urar wucin gadin dai tana iya bada kariya ne ga makamai masu linzami ne masu gajere da kuma matsaƙaicin zango, ta hanyar yin anfani da wasu na'urorin dake ƙasar Turkiyya da kuma waɗanda ke kan manyan jiragen ruwan Amirka a tekun Bahr Rum, wadda kuma ake sarrafawa daga wata cibiyar dake garin Ramstein na ƙasar Jamus.

Ƙaddamar da na'urar ta zo ne duk kuwa da hannun rigar da ƙungiyar NATO ke yi da ƙasar Rasha akan manufar samar da ita, inda Rashar ta nemi samun tabbaci - a bisa doka na cewar ba wai don ita aka samar ba, kana Amirka ta ce ƙungiyar ta yi hakanne domin samun kariya daga harin da Iran ka iya kaiwa Turai ɗin.

ARCHIV - US-Präsident Barack Obama (Archivfoto vom 06.03.2009). Seit zehn Jahren halten die USA Terrorverdächtige auf ihrem Marinestützpunkt Guantánamo Bay in Kuba fest. Nach den Anschlägen vom 11. September 2001 hatte US-Präsident George W. Bush dort die Errichtung eines Internierungslagers angeordnet. Sein Nachfolger Barack Obama beschloss zwei Tage nach seinem Amtsantritt im Januar 2009, das Camp binnen Jahresfrist zu schließen. Es war zum Symbol für Folter und Willkür geworden. Aus Obamas Versprechen wurde nichts. EPA/TANNEN MAURY (zu dpa-Themenpaket Guantanamo) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: picture-alliance/dpa

Ƙudirin yin aiki tare domin kammala samar da na'urar

Sabuwar na'urar bada kariya ga Turai daga harin makamai masu linzamin dai za ta kammala ne a shekara ta 2020 ne bayan samar da wasu na'urorin da za ta yi aiki tare da su da za'a dasa a ƙasashen Romaniya da Poland, abinda kuma shugaban Amirka Barak Obama ya bayyana ƙudirin cewar ƙungiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen cimma wannan burin:

" Ya ce kamar dai yadda muka sadaukar da kawunan mu baki ɗaya wajen warware matsalolin tsaro na bai ɗaya da muke fuskanta, za mu ci gaba da haɗin kai wajen kaiwa gaci a bisa wannan manufar."

A ƙarƙashin shirin samar da na'urar bada kariyar kuma, ƙugiyar ƙawancen tsaron NATO ta sanya hannu akan yarjejeniyar samar da mutum mutumi na roba, wanda za ta yi anfani da shi wajen lalata bama baman da ake dasawa a gefen tituna da kuma samar da jiragen saman yaƙin da suke sarrafa kawunansu wajen yin sintiri da kuma ƙaddamar da hare hare ta sararin samaniya.

German Chancellor Angela Merkel delivers her speech during an election rally with Schleswig-Holstein's Christian Democratic (CDU) chairman and top candidate Jost de Jager (not pictured) in Kiel, April 18, 2012. State elections in Schleswig-Holstein will be held on May 6, 2012. REUTERS/Fabian Bimmer (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters

Jinkirta janyewar dakarun Faransa daga Afghanistan

A lokacin taron NATOn kuma shugaban Faransa Farancois Hollande ya yi anfani da damar wajen ganawa tare da shugaban Afghanistan Hamid Karzai inda ya jaddada gudummowar da Faransa za ta baiwa ƙasar sa ta fannin bayar da horo ga jami'an tsaronta a dai dai lokacin da take aiwatar da shirin janye dakarunta a wannan shekarar, kamar yadda ya yiwa Faransawa alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓe, alƙawarin da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce da kamata yayi Faransar ta jinkirta aiwatar dashi:

" Ta ce mu dai munso a ce Faransa ta ci gaba da kasancewa tare damu a cikin ƙawancen ISAF har wa'adin janyewar ta cika."

Dama dai NATO ta ajiye shekara ta 2014 ne a matsayin wa'adin kammala janye dakarunta daga Afghanistan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe