1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa kawancen Trump da Macron

Kersten Knipp RG
April 26, 2018

Masu sharhi na ganin kwalliya ta maida kudin sabulu game da ziyarar da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya kai Amirka duba da yadda shugabanin biyu sun nunawa duniya irin kyan alakar da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/2wj8b
USA Washington - Donald Trump trifft Emmanuel Macron
Hoto: Reuters/J. Ernst

Yayin wannan ziyara dai Shugaban Macron ya nuna sha'awar kulla dangantaka da Shugaba Donald Trump bayan da ya gayyace shi halartar kasaitacen bikin tuni da juyin-juya hali na Bastille da aka saba yi shekara-shekara a kasar ta Faransa hadi da zaman cin abinci a lokacin waccan ziyara da ya hada da iyalan shugabanin biyu, lamarin da za a ce shi ne mafarin kyakyawar hulda tsakaninsu. To sai dai duk da wannan, masana irinsu Jeff Rathke na aza ayar tambaya kan wannan dangantaka inda ya ke cewar ''meye tasirin kulla kawancen? Shugaba Macron ya yi kokarin ganin ya kulla dangantaka da Shugaba Trump, babu dai tabbaci ko hakarsa ta cimma ruwa''.

Washington Donald Trump empfängt Macron
Masharhanta na aza ayar tambaya kan sahihancin abokantaka tsakanin Trump da MacronHoto: Reuters/J. Ernst

Duk da yunkurin da Macron ke yi na ganin ya yaukaka dangantaka tsakanin kasarsa da Amirka, hakan bai hana shi fadin albarkacinsa ba kan matakin Trump a batutuwa da suka shafi ci gaban kasashen duniya don kuwa ya tabo batun yarjejeniyar nukiliyar Iran da Amirka wadda gwamnatin Trump ke barazanar janyewa inda ya bukaci shugaban da ya sake nazari kan batun sannan ya yi jan hankali kan yarjejeniyar sauyin yanayi da kuma rikicin Siriya da wasu batutuwa da dama da Trump ke son yin fatali da su, abinda ya sa ake shakku kan sahihancin aminci tsakanin shugabanin biyu.

Gaba daya dai masu sharhi na ganin ba wai alaka da duk wani shugaba ya iya kullawa da shugaba na Amirka ne zai iya tasiri ba illa yadda za a iya shawo kan kalubale kan mutunta yarjejeniyoyi da kasashen duniya karkashin shugabancin Trump don magance matsalolin da ake fuskanta.