1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa huldar dangantaka tsakanin Nijar da Amurka

Gazali Abdou Tasawa
March 16, 2023

Kasashen Nijar da Amurka sun yi alkawarin bunkasa dangantaka a tsakaninsu ta fannin tsaro da tattalin arziki don ci gaban al'umominsu

https://p.dw.com/p/4OoFX
Niger Niamey | Besuch US-Außenminister Anthony Blinken
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya kammala ziyarar aiki da ya kai kasar a ci gaban wani rangadi da ya soma a wasu kasashen Afirka da nufin karfafa huldar Amurka da kasashen Afirka a daidai lokacin da Rasha ke kara samun tagomashi a nahiyar. Batun yaki da ta’addanci da tattalin arziki da kuma raya dimukuradiyya na daga cikin muhimman batutuwan da ya tattauna da mahukuntan Nijar.

A jawabin da sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka ya yi a gaban manema labarai tare da takwaransa na Nijar, Anthony Blinken ya bayyana wasu daga cikin fannonin da Amurkar ke taimaka wa Nijar inda take kashe kudi kimanin biliyan dubu.
 
Da yake tsokaci kan batun huldar tsaro da ta hada Nijar da Amurka da ma sauran kasashen duniya a fannin yaki da ta’addanci , Ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi Massaoudou ya bayyana tsarin da Nijar ke tafiyar da huldar.
 

Wannan ziyara ta Mistan Blinken ita ce ta farko a cikin shekaru 40 da Nijar ta samun ziyarar wani babban jami'in gwamnatin Amirka mai wannan matsayi. A lokacin wannan ziyara Mista Blinken zai tattauna da shugaban kasar ta Nijar Mohammed Bazoum kan karfafa huldar diplomasiya da ta tsaro tsakanin kasashen biyu. To sai dai Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen ya ce abin da suke jira daga wannan ziyara ta Mista blinken shi ne kawo gyara ga tsarin huldar Amurka da kasashen Afirka 

A karshen ziyarar Anthony Blinken ya sanar da taimaka wa Nijar da tallafin kudi miliyan dubu 50 na CFA domin taunkarar matsalar 'yan gudun hijira na ciki da wajen kasar da ke da zama a kasar. Sannan kasashen biyu sun jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine kan mamayar da Rasha ta yi mata