1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauye-sauyen Jamus a kan sha'anin tsaro

March 3, 2022

Jamus ta yi wa manufofinta kan sha'anin tsaro garanbawul bayan da Rasha ta kai hari kan Ukraine. Gwamnati ta ware karin Euro biliyan dari ga rundunar sojin kasar ta Bundeswehr.

https://p.dw.com/p/47xMQ
Litauen | Bundeswehrsoldaten des Nato-Gefechtsverbandes in Rukla
Hoto: Mindaugas Kulbis/AP/dpa

Gabannin wannan lokaci da Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi sanarwar ba zata ta karin Euro biliyan 100 ga rundunar Bundeswehr, sojojin na da burin samun jiragen yaki na zamani samfurin F-35 wanda babu sama da shi a yanzu. Dama dai rundunar ta Bundeswehr ta dade tsawon shekaru ta na nazarin sabunta jiragenta samfurin Tornado. Jawabin shugaban gwamnatin Olaf Scholz ya kasance tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama: Ya ce ''Jirgin samfurin F-35 an yi la'akari da shi ne bisa kasancewa jirgi ne da zai iya tashi daga kan jirgin ruwan yaki."

Jamus na kara karfafa rundunar sojojinta bayan da Rasha ta mamaye Ukraine

Berlin | Sondersitzung des Bundstags zur Krise in der Ukraine - Olaf Scholz
Olaf Scholz Shugaban gwamnatin JamusHoto: FABRIZIO BENSCH/REUTERS

Sayen sabbin jiragen yakin  samfurin F-35 zai ci tsabar kudi dubban miliyoyin Euro. Kudaden da ake da shi a ajiye kafin Rasha ta afka wa Ukraine sun sa Jamus sauya manufofinta kan tsaro: Ya ce: ''Muna bukatar jirage da za su tashi da jiragen ruwan yaki da kuma zaratan sojoji da suka sami horo domin tunkarar aikinsu gadan gadan."

Wannan jawabi na Olaf Scholz ya burge ba ma kawai 'yan majalisar dokoki ba, har da kwararrun masana kan harkokin tsaro, saboda jam'iyyarsa ta SPD ta sha hawa kujerar naki waje hana sayen tarin makamai a zamanin gwamnatin hadaka ta Angela Merkel har zuwa shekarar 2021.Tun bayan karshen yakin cacar baka rundunar Bundeswehr ta Jamus ta cigaba da raguwa da kuma kanfar kayan aiki. A yanzu an shirya aiwatar da gagarumin sauyi kamar yadda Ministan kudi Christian Lindner na Jam'iyyar FDP yake cewa:''Manufar mu ita ce cikin shekaru goma masu zuwa za mu samu samar da sojoji kwararru mafiya gogewa a Turai kuma sojoji mafi nagartar kayan aiki a Turai wadanda suka dace da muhimmancin da Jamus take da shi da kuma kimarta tarayyar Turai."

Jamus ta ware kashi biyu cikin dari na dukkan abin da ta samu a shekara don inganta tsaro

Deutschland | KSK-Bundeswehrsoldaten bei einer taktischen Vorführung
Hoto: Björn Trotzki/imago

Lindner yana fatan zuwa tsakiyar watan Maris a shigar da Euro biliyan dari din a cikin kasafin kudi na musmaman na 2022. Bugu da kari Jamus din za kuma ta ware kashi biyu cikin dari na dukkan abin da ta samu a shekara don inganta tsaro kamar yadda wakilan kungiyar kawancen tsaro ta NATO suka zartar tuntuni. A baya dai sayen manyan makamai da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma jiragen ruwa ya sha samun cikas saboda yadda ake sauya kasafin kudin daga shekara zuwa shekara. A saboda haka rundunar ta Bundeswehr ba ta iya yin shiri na dogon zango. A waje guda dai wasu kungiyoyin yan majalisar dokoki sun yi kashedi kan dawo da shirin yi wa kasa hidima ta aikin soji. An dai dakatar shirin a karkashin gwamantin CDU ta Angela Merkel a 2011.Rundunar ta Bundeswehr dai na bukatar karin sojoji. A yanzu dai kasar tana da sojoji 203,000 a cewar wani babban hafsan sojin kasar Janar Eberhard Zorn. Bayan yakin cacar baka, sojojin Jamus sun mayar da hankalinsu ne wajen aikin kiyaye zaman lafiya a waje misali a yankin Balkans da Afghanistan da kuma Mali.