Kara dagulewar al'amura a Siriya
March 26, 2012Talla
A sakamakon kara dagulewar halin tsaro a Siriya ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta sanar da rufe ofishin jakadancinta a Damaskus babban birnin kasar ta Siriya. Tun a makon da ya gabata ne dai ma'aikatar ta yi kira ga 'ya'yan Turkiya da ke zaune a Siriya da su gaggauta ficewa daga cikinta. Kenan Turkiya ta bi sahun kasashe da dama na Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka da kasashen Gulf guda shida wadanda tuni suka dauki wannan mataki. Tun wasu makonni kenan dakarun gwamnatin Siriya ke kai wa 'yan adawa hari. A cewar Majalisar Dinkin Duniya mutane sama da dubu 8 ne suka rasa rayukansu a rikicin na Siriya ya zuwa yanzu.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal